Shugaban kasa Mahammadu Buhari ya dawo gida Najeriya daga Adis Ababa babban birnin kasar Habasha.

 

Shugaba Buhari ya dawo Najeriya a yammacin yau Litinin bayan kwanaki hudu da yayi a Itofiya a wata ziyarar aiki.

 

Buhari ya tafi kasar Itofiya ne a ranar Alhamis din da ta gabata domin tattauna matsalolin da suka addabar kasashen yammcin Afirka.

 

Buhari da shuwagabbani kasar Itofiya sun tattauna batutun rashin tsaro harkokin tattalin arziki da kuma alamuran da suka shafi harkokin siyasa.

 

Sannan ana tunanin shugaba Buhari yaje kasar Itofiya ne domin samun shawarwari game da zabe ganin yadda saura kwanki biyar a gudanar da zabe a Najeriya.

 

Ana tunanin shugaba Buhari bayan dawowarsa daga zai iya fuskantar wahalar da yan Najeriya ke fama da ita ya janye maganar sauya kudi dake damun yan kasa a yanzu.

 

Cikin hotunan da suke yaduwa an hango shugaba Mahammadu Buhari yayin dawowarsa daga kasar Itofiya a filin tashin jirgi na Nmandi Azikwee da ke babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: