Hukumar ƴan sanda a jihar Kebbi ta kama wasu ɓata gari ɗauke da takardun sababbin kuɗi na bogi.

 

Hukumar ƴan sandan ta samu nasarar kama mutanen guda uku ɗauke da tsaɓar takardun sababbin kuɗi har na naira miliyan goma sha bakwai .

 

Ƴan sandan sun samu nasarar cafke ɓata garin ne a yankin Warrah cikin jihar Kebbi dake a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

 

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora, shine ya tabbatar da kama ɓata garin.

 

Kwamishinan ƴan sandan na jihar ya bayyyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a tashar mota ta Warrah a jihar Kebbi.

 

Ya kuma bayyana cewa ƴan sanda sun samu nasarar kama waɗanda ake zargin ne tare da taimakon mambobin ƙungiyar direbobin motoci ta ƙasa (NURTW) dake a tashar mota ta Warrah.

 

Ya bayyana sunan waɗanda ake zargin da Faruku Zubairu, Ibrahim Musa da Salisu Mohammed, waɗanda suka fito daga ƙauyukan Gungun Tawaye da Chupamini a ƙaramar hukumar Ngaski ta jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: