Aƙalla baankuna goma aka ƙona tare da lalata kayayan aikin su sanadin zanga-zangar nuna fushin ƙarancin sabbin kuɗi.

Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta tabbatar da haka ta ce wasu fusatattun matasa sun ƙona bankunan yayin da su ke zanga-zanga ranar Litinin.
Al’amarin ya faru a Sagamu a jihar Ogun.

A wasu yankunna birnin jihar, matasan sun ƙona tayoyi a manyan titunan garin don nuna fushi a dangane da ƙarancin sabbin kuɗi.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Muyiwa Adejobi ya bayyana ɗanyen aikin a matsayin ta’addanci da ɓarna.
A ranar Talata ma sai da gwamnan jihar Dapo Abiodun ya ziyarci wasu wuraren da aka yi aika aikar, da nufin jajantawa.
Sai dai a yayin zanga-zangar ba a ras arai ko guda ba.
Sanna ya buƙaci jama’a da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum domin a yanzu komai ya daidaita bayan kulawar jami’an tsaro.