Sakamakon karatowar babban zabe a ranar Asabar mai zuwa, tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya bukaci yan Najeriya da su zama yan kishin kasa, masu zaman lafiya yayin zabar yan takarkarunsu.

Ya fadi hakan ne a sakon da ya fitar ranar Talatar da ta gabata, sannan ya bukaci yan siyasa da su guji rigingimu dan ginawa da tabbatar da dimokuradiyya a kasar.
Jonathan yace ga matasa “kune manyan gobe, kar Ku bari a yi amfani da ku wajen tayar da fitintinu. Najeriya taku ce ku yakamata ku gina ta.”

Sannan kuma ya kara da cewa “ga dukkan yan kasa wannan lokacin gaskiya ne da kwarin guiwa, dimokuradiyya ta sanya mana kadadararmu a hannunmu ta bamu karfin da zamu zabi abinda muke so. Dan mu kudurce gobenmu da kuma saita ta.”

“Na bukace ku da kuyi zabin da ya dace da kasarmu, mu yi zabe cikin lafiya sannan mu girmama ra’ayi da zabin juna” Jonathan din ya fada.
A karshe ya nuna yadda zaben yake da muhimmanci ga yan Najeriya, kuma ya bayyana ta a matsayin lokacin gaskiya da kwarin guiwa.