Kungiyar hadakar matasan Arewa sun nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a zaben da za’a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Sun ce tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar shine zabinsu, sakamakon gogewa da sanin makamar aiki da yake dashi na shugabanci tsawon shekaru.
Kungiyar mai dauke da shugabancin matasa 70 a jihohi 19 na arewacin Najeriya sun ce, sun zabi Atikun ne saboda dukkan yan takarkarun 18 yafi kowa sanin yadda za’a kawo cigaba da gina Najeriya.

Yayin bayani ga manema labari a Gidan Arewa jiya Laraba a Kaduna, shugaban hada taron Murtala Abubakar yace babu wani a cikin sauran yan takarkarun da ya gina tsarin siyasa ginshiku duk fadin Najeriya kamar Atiku.

Yace sun yanke shawarar ne bayan sun ji bayanai daga kungiyar dattawan Arewa, kungiyar tuntuba ta Arewa da sauran rukunan Arewa akan takarar ta Atiku Abubakar.
Sannan ya bukaci yan Najeriya da suyi tururuwa su fito su zabi Atikun, tare.da fadin cewa za’a tabbatar da shawarar ne.idan aka samu goyon baya.
A karshe Murtala yace, Atikun shine yafi sauran dadewa da rike ofisoshin siyasa, kuma duk yafi su sanin ciki da wajen Najeriya.