Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikinn kasa zagon kasa EFCC ta bayyana cewa ‘yan siyasa na rike da kudi sama da naira biliyan dari biyar na tsoffin kudi wanda ba’a mayar babban bankin Najeriya ba.

Shugaban Hukumar Abdulrashid Bawa shine ya bayyana haka ta cikin shirin siyasar mu a yau na gidan talabijin na Channels.
Ya bayyana cewa hukumarsa ta sami bayanai da ke nuni da cewa ‘yan siyasa na shirin yin amfani da wasu hanyoyi domin sayan kuri’a a lokacin zabe.

Ya kara da cewa ‘yan siyasar basu da wata mafita illa sayan kuri’a domin sunga cewa na’urar BVAS za ta kawo masu cikas.

Bawa ya cigaba da cewa yana mai farin cikin cewa hukumomin tsaro zasu yi aiki tukuru wajen ganin an gudanar da zabe lafiya a fadin Najeriya.
Shugaban na EFCC ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su baiwa hukumar hadin kai a kokarinta na yaki da masu sayan kuri’u a ranar zabe.