Akalla mutane 15 ne su ka rasa rayukansu yayin da bakwai su ka jikkata a wani hadarin mota da ya afku a kauyen Nabordo da ke karamar hukumar Toro ta Jihar Bauchi.

Babban kwamandan hukumar ta FRSC Mista Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan a jihar Bauchi.


Kwamandan ya ce motoci biyu ne su ka yi arangama yayin da mutane 22 lamarin ya rutsa da su wanda su ka hada da maza 18 mata biyu da kuma yara biyu mace da namiji.
Mista Yusuf ya bayyana cewa maza 12 da babbar mace daya da yara biyu a yayin hadarin.
Kazalika ya ce mutane bakwai sun jikkata, inda aka aike da su Asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Jihar domin Kula da lafiyar su.
Mista Yusuf Abdullahi ya kara da cewa wadanda su ka rasa rayukan su an mika gawarwakin su zuwa Asibiti.
Kwamandan ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Alhamis sakamkon gudun wuce sa’a da direbobin ke yi.
Sannan ya bukaci masu tuka ababan hawa da su guji gudun wuce sa’a tare da bin dokokin tuki da kuma tabbatar da ingancin tayoyi a yayin tafiya.