Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa kimanin mutum 87,209.007 ne suka karbi katin zabensu na din-din-din a fadin Najeriya.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin da yake bayani ga ‘yan jaridu a helikwatar hukumar da ke birnin Abuja.
Tunda fari dai hukumar ta sanya ranar 12 ga watan Disamba zuwa ranar 22 ga watan Janairu a matsayin ranakun da jama’a za su karbi katinan zaben su a duk-kan ofisoshin hukumar na kananan hukumomi 774 na fadin kasar.

Sai dai hukumar ta sake kara wa’adin zuwa ranar 5 ga watan Fabrairu ,daga bisa kuma bayan karewar wa’adin hukumar ta sake rufe karbar katunan.
