A yayin da ya rage kasa da kwana daya a gudanar babban zaben a Najeriya Rundunar ‘yan sandan Jhar Rivers ta kama wani dan majalisar tarayya mai suna Dakta Chinyere Igwe dauke da makudan kudade kasar waje wanda ba a san adadin su ba.

Jami’an sun kama Dakta Igwe ne da ke wakiltar mazar Port-Harcourt na Biyu a majalisar tarayya da sanyin safiyar yau Juma’a a Aba Road a Port-Harcourt a Jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Punch.

Jami’an da aka turasu hedkwatar hukumar zabe da ke Jihar a Aba Road,a lokacin da su ke binciken ababan hawa da su ka gudanar da misalin karfe 2:45 su ka kama dakta Chinyare dauke da kudade a cikin wata jaka a motar sa wanda yawansu ya kai kusan dala 498,100.

Bayan kamashi an kuma gano sunayen wadanda za a rabawa kudade a lokacin zaben.

AIG Abutu Yaro FDC ya bayar da umarnin gudanar da bincike akan sa tare da gurfanar dashi a gaban kotu domin yi masa hukunci.

Rundunar ta yi kira ga ‘yan takarkaru da jam’iyyun siyasa da su yi biyayya ga dokokin zabe.

Rundunar ta kuma bai’wa al’ummar Jihar lambobin wayar da za su kira hukumar idan sun ga ana aikata ba daidai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: