Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a Abubakar Malami SAN ya ce Shugaba Buhari bai karya umarnin kotu koli ba akan batun sauya fasalin naira na babban bakin Najeriya CBN.

Abubakar Malami ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron manema labarai kashi na 67 wanda ya gudana a birnin Abuja.

Malami ya tabbatar da cewa Shugaba Buhari bai yi karan tsaye ga babbar kotun Najeriya ba kamar yadda wasu suke zargi.

Kan batun sauyin fasalin kudade ankai ruwa rana tsakanin gwamnatin tarayya da wasu gwamnonin Jihohin kasar da suka hada da gwamnonin Kaduna, Zamfada da kuma Kogi,sai dai bayan da gwamnonin uku suka shigar da kara kotune Karin wasu gwamnonin suka biyo bayan su.

Idan za’a iya tunawa dai gwamnan babban bankin Najeriya ya kara wa’adin amfani da tsoffin kudi a fadin kasar har zuwa ranar 10 ga watan fabrairu daga ranar 1 ga watan kamar yadda aka tsarayi tun a baya.

A satin daya gabata anjiyo Shugaba Muhammadu Buhari na baiwa babban bakin kasar umarnin sake Samar da takardun kudi na naira 200 a dukkan fadin kasar, tare da bayar da umarnin cigaba da amfani da takardar naira 200 har zuwa kwanaki 60 masu zuwa.

Kawo yanzu dai ‘yan Najeriya na jiran ranar 5 ga watan Maris domin yanke hukunci kamar yadda babbar kotun kasar ta bada umarni.

Sai dai abin tambayar shin takardun kudi na naira 500 da kuma naira 1000 na iya yin aiki a Najeriya ko kuwa? Wannan shine babbar tambayar da ‘yan Najeriya ke dakon jin amsoshin ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: