Wasu batagarin matasa a Jihar Borno sun kaiwa tawagar motocin gwamnan Jihar ta Borno Babagana Umara Zulum hari a garin Maiduguri da ke Jhar.

Masanin tsaro a yankin tafkin Chadi Zogazola Makama ya bayyana cewa lamarin ya farune a yammacin ranar Alhamis.


Makama ya rawaito cewa matasan sun kaiwa tawagar gwamnan harin ne a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta dawowa daga mahaifar sa Mafa da ke Jihar.
Zogazola ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter,inda ya ce koda a makwannin da su ka gabata sai da aka kaiwa tawagar matar gwamnan hari Hajiya Fatima Zulum a Dalori da ke cikin karamar hukumar Konduga da ke Jihar inda aka lalata mutoci takwas.
Makama ya kara da cewa matasan da ke unguwar Kaleri a Maiduguri ne su ka yi aika-aikar inda su ka lalata motocin tawagar uku.
Wata majiya ta bayyana cewa motocin da aka lalata sun hada da motar injiniyoyi manema labarai tare da wata mota guda daya.