Ana zargin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karya dokar zaben da ya sanya wa hannu a bainar jama’a ta hanyar nuna abin da ya zaba a zaben shugaban kasa na 2023.

 

Bayan Buhari ya kada kuri’arsa a akwatin zabe mai lamba 003 a mazabarsa ta Sarkin Yara da ke mahaifarsa a Daura Jihar Katsina, sai ya daga katinsa na jefa kuri’a yana nuna wa duniya.

 

Hakan da ya yi ya saba da Dokar Zaben ta 2022 da majalisar dokoki ta kasa ta yi wa kwaskwarima, shi kuma ya sanya hannu ta zama doka a shekarar 2022.

 

Sashe na 129 (1) na Dokar Zaben ya ce, nuna duk wani abu da ke alamanta jam’iyya ko mai alaka da zabe a wurin da ake yin zabe ko tattara sakamakon zabe laifi ne da zai jawo wa wanda ya aikata tarar N100,000 ko kuma daurin wata shida a gidan yari.

 

Hakan da ya yi haramun ne a karkashin Dokar Zaben ta 2022 da majalisar dokoki ta kasa ta yi wa kwaskwarima, shi kuma ya sanya hannu ta zama doka a shekarar 2022.

 

Wannan ne dai karon farko da Buhari ya kada kuri’a a matsayin dan kallo tun bayan da a fara zawarcin kujerar shugaban kasa a 2002, shekara 20 da suka gabata.

 

A ranar 29 ga watan Mayu, 2023 Buhari zai mika mulki bayan ya kammala wa’adi biyu na shekara akwas da ya fara a shekarar 2015

Leave a Reply

%d bloggers like this: