Bayan kammala zaɓukan shugaban ƙasa dana yan majalisar tarayya dana Sanatoci, yanzu haka sakamakon jihohi dana mazaɓu sun soma kammaluwa.

 

Tuni jam’iyyu suka soma sanin makomar su tare da sanin wace irin rawa suka taka.

 

Wasu jam’iyyun sunyi abinda ake zato na samun ƙuri’u masu rinjaye a wajajen da suka fi rinjaye.

 

A yayin da wasu kuma sukayi faɗuwar baƙar tasa.

 

Watakila hakan bai rasa nasaba da yadda sakamakon yazo musu da mamaki, al’ajabi tare da bazata.

 

Wasu jam’iyyu na ganin sakamakon jam’iyyun suna zuwa ne a salon aringizo , wanda hakan ke kawo shakka akan alƙaluman zaɓukan.

 

Shakkar ce tasa jam’iyyar Labor Party wacce aka fi sani da LP tayi kira ga INEC data gaggauta sauke zaɓen shugaban ƙasa da akayi jiya.

 

Ɗaya daga cikin dalilin da jam’iyyar Labor Party ta bayar shine, akwai buƙatar a sauke zaɓen tunda INEC ɗin taƙi ɗaura sakamakon zaɓen a matattarar bayanai ta INEC a yanar gizo.

 

Shugaban jam’iyyar na ƙasa ne Julius Abure ya bayyana haka a wani saƙo daya rabawa manema labarai, inda tace INEC tasoma saka shakku a cikin zuƙatar al’umma biyo bayan gaza yin haka.

 

Abure yace, ƙin da INEC tayi na ɗaura sakamakon zaɓe awa goma sha biyu bayan kammala zaɓe abu ne mai cin rai kuma, ba komai bane face fashi da makami irin na siyasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: