Malam Ibrahim Shekarau shi ne wanda aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata na mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.

Hukumar INEC ta bakin malamin zaben shiyyar jihar Kano ta tsakiya, Farfesa Tijjani Hassan Darma ta ce jam”iyyar NNPP ta ci zabe.


Farfesa Tijjani Hassan Darma ya ayyana sunan Ibrahim Shekarau a matsayin ‘dan takaran da ya yi galaba a kan sauran jam’iyyu da kuri’u 456,787.
Wanda ya zo na biyu a zaben shi ne Abdulkarim Abdussalam Zaura na APC mai kuri’u 168, 677.
Ibrahim Shekarau wanda yanzu ‘dan jam”iyyar PDP ne sun sha kashi a zaben, ‘yar takarar jam’iyyar PDP wato Laila Buhari ta zo ta uku ne a zaben na bana.
Matsayar da hukumar zabe ta kasa ta bada ya jefa al’ummar Kano cikin wani irin hali ganin cewa su na hango Sanata Rufa’i Sani Hanga a majalisa.
Sanata mai ci Ibrahim Shekarau ya na cikin wadanda suka shiga jam’iyyar NNPP da farko, amma sai daga baya ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Sauya-shekar da tsohon
Gwamnan ya yi ya jawo ya salwantar da takarar Sanata da aka ba shi, kuma ya sanar da INEC cewa ya fasa shiga zabe.
Duk da wasikar da tsohon Ministan ilmin ya rubuta, hukumar zabe ba ta canza sunansa a matsayin ‘dan takara ba, wannan ya jawo NNPP ta shiga kotu.
Kwamitin yakin neman shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP ya yi kira ga hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta ta soke dukkan sakamakon da aka sanar kawo yanzu.
Mai magana da yawun kamfen, Daniel Bwala ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar yau Talata.
Sun bukaci a dakatar da tattara zaben yanzu kuma a bada amsa game da korafe-korafen da jam’iyyu sukayi game da kin amfani da na’urar BVAS da sauya sakamako a yanar gizo.
Ya kara da cewa a zabi sabon ranar gudanar da zabe a wadannan wurare kuma a tabattar da cewa an dora sakamakon, wajibi ne a yi amfani da BVAS kan a ce anyi zabe na gaskiya.
Sun buƙaci a yi watsi da dukkan sakamakon da aka sanar har zuwa lokacin da aka dora dukkan sakamako daga runfunan zabe zuwa yanar gizon INEC, kuma a sanar da su, kuma a baiwa wakilun jam’iyyu nasu kwafin.