Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Gregory Obi, ya samu nasara a zaben babbar birnin tarayya FCT Abuja.

 

A sakamakon karshe da aka tattara, LP ta samu kuri’u 281,717 da ta kayar da dan takarar APC, Bola Tinubu, da ya samu kuri’u 90,912 sai kuma PDP ta samu kuri’u 74,193.

 

Nasarar Obi ta bayyana ne bayan kammala kirgen kuri’u a manyan hukumomin Abuja guda shida.

 

Ya lallasa Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.

 

Zaku tuna cewa jam’iyyar PDP ce ta shahara da lashe zabe a Abuja, amma wannan karon na uku ta zo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: