Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da Bola Ahmed Tinubu a matsyain wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Sabon shugaban ƙasar ya samu nasara da mafi rinjayen ƙuri’u 8,794,726 daga cikin ƙuri’u 24,025,940 da aka kaɗa.

Shugaban hukumar zabe na ƙasa Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da zaɓen bayan tattara saakamakon zaɓen a ɗakin tattara sakamakon da ke Abuja.

Ɗan taakarar shugaban ƙasar daa ke biye masa da yawan ƙuri’u Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u 6,984,520.

Sai na uku na jam”iyyar LP ya smau ƙuri’u 6,101,533 yayin da Rabi’u Kwankwaso na jam”iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 1,496,687.

Tuni aka miƙa sakamakon zaben ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da mataimakinsa bayna cika dukkan ƙaidaar doka.

Sai dai jam’iyyun LP daa PDP sun yi watsi da sakamakon tare da buƙatar shugaban hukumar zaɓe ya sauka daga kujerarsa.

Bola Ahmed Tinubu shi ne shugaban Najeriya na biyar bayan kafa mulkin farra hula daga shekarar 1999.

Leave a Reply

%d bloggers like this: