Wata kotun Majistire dake zamanta a jihar kano ta aike da Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tudun-wada da Doguwa a zauren majalisar kasa zuwa gidan ajiya da gyaran hali.

Ana zargin Doguwa da aikata laifuka da suka hada da kisan kai tare da mallakar makami ba bisa ka’ida ba.
An gurfanar da Dan Majalisar tare da wani mutum Wanda ake zargin sun hada kai wajen tayar da zaune tsaye tare da kisan kai a yankin karamar hukumar Tudun-Wada, a ranar asabar da ta gabata.

Sai dai alkalin kotun ya dage cigaba da sauraron shari’ar har zuwa 7 ga watan Maris da muke ciki, domin duba yuwuwar bayar da beli ko akasin haka.
