Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa yau a Abuja.

Zaman majalisa na farko ke nan da aka yi bayan sanar da nasarar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu.

An gudanar da zaman a far gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Zaman ya samu halartar saakataren gwamnaatin tarayya Boss Mustapha da shugaban ma aikata sai mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro Babagana Monguno.

Sauran ministoci da su kaa halarci taron akwai ministar jin kai, da ministar kasafi da tsare-tsare sai ministan kasuwanci da zuba hannun jari.

Haka kuma kawa ministan kimiyya da fasaha, da kuma ƙaramin ministan man fetur Timipre Sylva.

Leave a Reply

%d bloggers like this: