wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun harbe wani tsoho har lahira a lokacin da yake tsaka da aiki a gonarsa a jihar Neja.

Wata ‘yar uwa ga marigayin ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun budewa dattijon mai suna Samanja wuta ne a lokacin da ya ke yin shuka a gonarsa ta noman rani, a kauyen Baje-Patiko da ke karamar hukumar Munya ta jihar Nija.

Ta cigaba da cewa saboda da hare-haren ‘yan bindiga yawancin mutanen kauyukan da ke yankin sun bar gidajensu domin yin gudun hijira a Sarkin Fawa da ke zaman helikwatar karamar hukumar ta Munya.

Ta kara da cewa Marigayin Samanja na zuwa gonar tasane da garin sarkin fawa domin samarwa iyaansa abinci.

‘yar uwar marigayin ta tabbatar da cewa jami’an sakai sunje gonar domin dauko gawar mamacin a safiyar talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: