Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayar umarnin sauke shugaban hukumar sufuri na Jihar KSTA Alhaji Bilyaminu Muhammad Rimi daga kan mukaminsa.

Sakataren gwamnan Jihar Alhaji Mukhtar Lawan shine ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Sakataren ya bayyana cewa korar da aka yiwa shugaban hukumar ta sufuri ta fara aiki ne nan take.

Muntari Lawan ya kara da cewa gwamnan Jihar ya kuma nada Alhaji Gambo Abdulkadir Rimi a matsayin sabon shugaban hukumar.

Gwamnan na Katsina ya kuma sake sallamar Alhaji Tasi’u Dahiri dan Dagore kwamishinan ayyuka da gidaje na Jihar daga bakin aiki a ranar Litinin din da ta gabata.

Sannan gwamnan ya sake korar wasu ma’aikata da su ka hada da Hajiya Fatima Ahmad wadda ta kasance sakatariyar cimma muradun karni da shugaban hukumar jindadin Alhazai na Jihar Alhaji Yusuf Barmo da kuma sakataren noma da albarkatun kasa Alhaji Aminu waziri.

Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa korar da gwamnan yayi musu na zuwa ne a wani bangare na yin garanbawul ga gwamnatinsa.

Wata majiya mai tushe daga gidan gwamnatin Jihar ta bayyana cewa korar gwaman yayi musu na da nasaba da shan kayen da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu yayi a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: