Wasu da ake zargin masu satar man fetur ne sun rasa rayukan su a yayin tashin gobara a lokacin da su ke kokarin satar man a bututun man gwamnati a Jihar Rivers.

 

Daraktan cibiyar wayar da kan matasa da yanayi Fyneface ne ya bayyana hakan a jawabin da cibiyar ta yi a shafin ta na COSAS.

 

Wadanda su ka rasa rayukannasu ana zargin su na satar danyen man ne tare da tacewa.

 

Fyneface ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2 na daren ranar Juma’a a lokacin da wani direba ya tayar da daya daga cikin motocin da ake amfani da su wajen satar danyen Man.

 

Ya kara da cewa ana amfani da motar ne wajen tafiyar da man sata zuwa cibiyoyin tace danyen man na bayan fagge.

 

Fyneface ya bayyana cewa gobarar ta haddasa a sarar rayukan mutane da dama tare da babura da motoci.

 

Rohotanni sun bayyana cewa wadanda su ka mutu a masu dibar man ne tare da lodin shi a cikin mota.

 

Bayan faruwar lamarin an aike da jami’an soji da na ‘yan sanda zuwa gurin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: