Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta gurfanar da wani matashi dan kasuwa mai suna Khalisu Ahmad mai shekaru 20 bisa zarginsa da satar kayan sawa da kuma huluna na naira 250,000.

Jami’an sun gurfanar da matashin ne a kotun Dei-Dei da ke birnin na Abuja a ranar Alhamis.


Matashin wanda ya kasance mazaunin Angwa Danladi zuba da ke aikata ta’addanci tare da haurawa gida da kuma aikata sata.
Dan sanda mai gabatar da kara Olanipekun Babajide ya bayyanawa kotun cewa an kai karar wanda ake zargin ne tun a ranar 12 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Dan sandan ya ce matashin ya shiga gidan wani mai suna Abdulrahman Dauda da ke Fruist Market Dakwa a Abuja tare da yin sata a gidan.
Dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana cewa laifin ya saba da sashe na 79 da 348 da kuma 288 na kundin Penal Code.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta zargin da ake yi masa.
Alkalin kotun Malam Saminu Sulaiman ya bayar da belin wanda ake zargin akan kudi naira nairab 100,000 tare da kawo mutum daya wanda zai tsaya masa.
Alkalin ya dage sauraran shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Maris din da mu ke ci.