A yau Asabar ne aka yi bikin nadin sabon sarkin dutse a garin Dutse dake jihar Jigawa.

A yau aka nada Alhaji Hameem Nuhu Mahammadu Sunusi a matsayin sabon sarkin Dutse a jihar Jigawa.
Sarkuna daban daban ne suka hallarci bikin nadin a yau dama masu fada a ji daga kasar.

Bayan rasuwsar tsohon sarkin Dutse Dr Nuhu Mahammadu Sunusi ya sha fama da matsananciyar rashin lafiya wanda ya mutu ya na da shekaru 78 a takaice kamar yadda jaridar Daily Post ta rawaito.

An kawo sunayen yayan sarkin biyar wadanda ake saran daga cikin su ne za a samu wanda zai gaji sarautar Dutse.
Sai dai a irin na su duban da suka yi sun gano cewa Hamem Nuuhu shi ne zai gaji sarautar gargajiyar garin Dutse kamar yadda aka bayyana.