Shugaban kasa Mahammmadu Buhari ya isa babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da shwagabanniin kasashe biyar.

Mahammdu Buhari ya sauka a kasar ta Qatar wadda yanki ne na labarawa a yau Asabar domin tattauna batun kasa Najeriya.

Mataimakin Mahammadu Buhari a fannin yada labarai labarai malam Garba Shehu shi ne ya bayyan haka inda ya ce buhari ya samu gayyata daga sarkin Qatar a Sheik Tamim Bin Hamad Al thani.

Buhari zai je kasar Qatar ne domin tattauna batutuwa da dama wadanda suka hada da batun tsaro tattalin arziki da yunwa da dai sauransu wanda za fara tatttaunawa daga gobe biyar zuwa 8 ga watan maris.

Garba shehu ya ce sannan za a yi duba da irin damuwa dake damun kasashe irin Najeriya domin gudu daya da tsira daya.

Shugaba Buhari ya samu yar rakiyarsa na ministoci wadanda za su raka shi domin karbar wannan gayyatar.

Amma ana saran shugaba mahammadu Buhari zai dawo gida Najeriya a ranar Laraba takwas ga wata kafin ranar Asabar zaben gwamnoni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: