Yanzu Alkalin kotu ya ba da belin Hon. Ado Doguwa, wani jigon siyasar APC kuma dan majalisar tarayya daga jihar Kano.

 

A baya an tsare Doguwa ne bisa zarginsa da hannu a mutuwar wasu mutane a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a Kano.

 

An tsare Doguwa na tsawon kwanaki biyar bayan da ‘yan sanda suka gurfanar dashi a gaban kotun majistare da ke Kano.

 

Sai dai, lauyan Doguwa, Nureini Jimoh (SAN), ya nemi belin wanda yake karewa daga alkalin kotun, Muhammad Nasir Yunusa.

 

A cewar Jimoh, tun da an ce ana zargin Doguwa da hannu a kisan kai da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, kotun majistare bai da hurumin yin shari’ar.

 

Bayan sauraran batutuwa, mai shari’a Yunusa ya ba da belin Doguwa tare da ba shi sharadin kawo mutum biyu masu tsaya masa.

 

Hakazalika, ya ce daya daga cikin masu tsayawa dan majalisar dole ya kasance basaraken gargadiya daya kuma ya kasance sakataren dindindin a ma’aikatar gwamnatin tarayya ko ta jiha.

 

Har ila yau, ya umarci Doguwa da ya kawo takardunsa na ketare kasa, wanda kotun zai ba shi duk lokacin da ya bukaci barin kasa.

 

Kuma an ce, dole ya dawo da takardun bayan dawowa daga duk wata tafiya da ya yi a wajen kasar.

 

Daga karshe, kotun ya bukaci Doguwa da ya nesanta kansa da mazabarsa a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisun jiga da ke tafe a ranar Asabar mai zuwa.

 

Idan baku manta ba, a ranar 1 ga watan Maris ne aka tasa keyar Ado Doguwa zuwa magarkama bayan zaman kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: