Dan wasan da ke kan gaba wajen jefa kwallo a gasar Siriya A ta kasar Italiya Victor Osimhen yace, yana mafarkin taka leda a gasar firimiyar kasar Ingila.

Dan wasan gaban kasa Najeriyar wanda ya kasance a Birnin Rum dan karbar kyautar zakakurin dan wasa daga haure, yace yana son kawo Babbar gasa ga Kungiyarsa ta Napoli kuma yana son ya d’an gusa.
“Da yawan mutane suna ganin gasar firimiyar Ingila a matsayin babbar gasa mafi girma a Duniya.” Osimhen ya fada.

Kuma ya kara da cewa “yanzu ina cikin daya daga manyan gasoshi na Duniya, wato Siriya A ta Italiya.”

“Kwarai dagaske ina yin dukkan mai yiwuwa dan cimma buri na na bugawa a gasar Firimiya wata rana, amma komai zuwa yake kuma zan cigaba da kokari” in ji Osimhen.
Osimhen ya koma kungiyar Napoli ne a shekarar 2020, daga kungiyar Lille ta Faransa.
Yanzu haka ya jefa kwallaye 19 a wannan kakar wasannin, kuma kungiyar Napoli ita ke jan ragamar jadawalin gasar da tazarar maki 15.