Masu ababan hawa a babban Birnin tarayya Abuja suna matukar kokawa, sakamakon matsin rashin man fetir da suke fama da shi wanda ya haifar da dogwayen layuka a gidajen mai.

Jami’in kamfanin dillancin labarai na kasa NAN da ya bibiyi gidajen mai a birin tarayya Abuja ya ruwaito cewa, da yawan gidajen man basa bayarwa, masu bayarwar kuma suna cike sun hada cunkoso.

Masu ababan hawan kuma sun bayyana rashin jin dadinsu game da rashin tsabar kudi a hannu, Wanda suka ce shima ya taimaka wajen haifar da matsalar, sannan sunyi kira gwamnati ta kai dauki.

Kamfanin Samar da man fetir na kasa NNPCL ya alakanta dogon layin a gidajen mai a Abujan da sauran bangarorin Najeriya, da takaituwar kasuwanci da zirga-zirga sakamon zaben shugaban kasa da yan majalissun tarayya da ya wakana.

Sannan NNPCL din sun ce, tuni an dawo bakin aiki a defo-defo da manyan motoci dan rarraba man zuwa sauran sassan Najeriya.

Wasu mazauna garin sun kuma koka da cewa, sun rasa man da zasu saka a injinan su dan su yi kasuwancinsu da yin bukatu a gidajensu.

NAN sun ruwaito cewa, ‘yan kasuwar bayan fage suna siyar da Lita goma na man a kan kudi naira dubu hudu idan zaka biya kudin ta banki, yayin da suke siyar da shi Naira dubu uku da dari biyar idan zaka biya tsabar kudi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: