Babban bankin Najeriya CBN yace bai bawa sauran bankunan kasuwanci umarnin cigaba da raba tsoffin takardun kudi ba, duk kuwa da umarnin da kotun koli ta bayar na cigaba da amfanin da tsoffin takardun kudin a tsakanin al’umma.

A zaman kotun sauraran karar na Alkalai 7 wanda mai shari’a Inyang Okoro ya jagoranta a ranar juma’ar da ta gabata, ta bayyana cewa baya bisa tsarin doka umarnin da Shugaba Buhari ya bayar ga CBN na sauya fasalin takardun kudin na 200, 500 da 1000.

Kotun ta bayyana cewa baya bisa ka’idar kundin tsarin mulki bayar da umarnin ba tare da tuntubar johohi, jami’an gwamnatin tarayya da kuma sauran masu ruwa da tsaki ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa akwai rudani ga bankunan kasuwanci da saurarn harkokin kasuwancin, sakamakon rashin bayar da umarni daga babban Bankin na cigaba da karbar tsoffin takardun kudin.

Daily Trust din ta ruwaito cewa mai magana da yawun bankin na CBN Isa Abdulmumin ya shaidawa wakilinta cewa, Bankin bai bayar da jawabi a hukumance akan cigaba da karbar tsoffin takardun kudin ba.

Tuni dai wasu daga cikin bankuna suka fara rarraba tsoffin takardun kudin ga abokanan huldarsu a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: