Dakarun sojin Najeriya sun ceto kwamishinar mata ta jihar Cross Rivers Misis Gertrude Nja daga hannun masu garkuwa da mutane.

Jami’in hulda da jama’a na sansani na 13 na rundunar sojan Kasar nan da ke birnin Calava Kaftin Dorcas Aluko, ta bayyana cewa kwammishiniyar na samun kulawa daga likitoci.

Ta kara da cewa Sojin sun yi wa masu karkuwa da mutanan kwanton 6auna ne a kusa da Peter Effiong Creek.

Ta ci gaba da bayyana cewa dakarun sun yi amfani da kwarewa wajen yiwa masu garkuwar kwanton 6auna tare da ruwan wuta, wanda hakan ya tilastamusu arcewa a inda daga bisa ni jami’an sojin kasar suka sami nasarar ceto kwamishiniyar.

Rahotanni sun bayyana cewa anyi garkuwa da kwamishiniyar ne tun a ranar 1 ga watan fabrairu a yankin anguwar Mayne Avenue, da ke Kalala ta Kudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: