Kasar Ukraine ta bayyana cewa an shafe daren jiya ana luguden wuta da makamai masu linzami a sassa daban-daban na kasar ciki harda birnin Kharkiv wanda ke yankin Odesa.

Tun da fari dai an jiyo karar makamai masu linzami a yankuna 13 na kasar ta Ukraine.

Idan dai ba a manta ba, ba wannan ne karon farko da kasar ke fuskantar lungden wuta ba daga makwabciyar ta Kasar Rasha, don ko a makwan jiya ma sai da kasashen G20 suka gudanar da taro a kasar India domin duba yuwuwar cigaba da taimakawa kasar a luguden wuta da ta ke sha daga Rasha, in da ake ganin hakan zai taimaka wajen mayar da kasar baya ta fuskar cigaba.

Bayanai sun bayyana cewa gwamna Kharkiv Oleg Synergubov, ya sanar da cewa hare-haren 14 sun rusa wani ginin farar hula tare da lalata ababen more rayuwa a yankin.

A nasa 6angaren gwamnan Odesa Makysm Marchenko, ya bayyana cewa an sami 6arna mai yawa sai dai babu asarar rai ko jikkata yayin harin na daren jiya laraba kamar yadda gwamnan ya tabbatar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: