Mata guda biyu sun rasa rayukansu sakamakon arangama da jirgin kasa yayi da motar ma’aikatan gwamnatin jihar Lagos, a Ikejan jihar Lagos yau Alhamis.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyana cewa, mutane da yawa sun jikkata sakamakon faruwar lamarin a safiyar yau.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mata guda biyu sun rasa rayukansu, sannan an fitar da wasu kuma da suka samu raunika.

Motar ma’aikatan tana kokarin tsallaka titin jirgin ne, yayin da shi kuma jirgin yake tahowa Lagos daga Abeokuta in da ya afka wa motar a kan titin jirgin.

Babban jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Lagos Olufemi Oke-Osanyintolu yace, bincikensu ya tabbatar hatsarin ya faru ne sakamakon sakacin matukin motar.
Ya kuma tabbatar da cewa mata guda biyu sun rasa rayukansu, sannan da yawa sun jikkata a faruwar lamarin.