Rundunar sojin Najeriya sun ce sun fara gudanar da bincike a kan sojan da ake zargi yaa hallka aabokan aikinsa sannan daga bisani ya kashe kansa.

Ana zargin wani soja ya harbe abokan aikinsa uku sanna ya harbe kansa daga bisani.

Lamarin ya faru a ƙaramar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

Mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Onyema Nwachikwu ya ce lamarin yaa faru a ranar Lahadi yayin da aka aike da jami’an don yin sintirin samar da tsaro a jihar.

Tuni babban kwaamanda mai kula da shiyyaa ta. Taakwas da wasu manyan jami’an su ka ziyarci wajen da lamarin ya faru.

Sannan sun roki sauran jami’an da su kasance masu mutunta juna, tare da ƙoƙarin sanar da hukumar halin rashin daɗi daa ke tsakaninsu.

Hukumar ta nuna damuwa a kan faruwar lamarin tare da ƙoƙarin ganin hakan ba ta skae faruwa ba a nan gaba

Leave a Reply

%d bloggers like this: