An tuhumi kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar Sifaniya, bisa zargin bayar da cin hanci ga kungiyar alkalan wasanni, wanda Barcelonan ta musanta.

Ana tuhumar kungiyar ne dai da laifin na bayar da cin haci dangane da wani biyan kudi da suka yi ga Jos Maria Enriquez Negreira, wanda shine tsohon mataimakin shugaban kungiyar alkalan wasannin kasar Sifaniya.

A watan da ya gabata an gano cewa kungiyar ta bawa Negreira da kamfaninsa kudi kimanin Yuro Miliyan 8 da dubu 400, a tsakanin shekarar 2001 zuwa shekarar 2018.

A Juma’ar da ta gabata ne dai aka sanar da kotu a Birnin na Barcelona cewa, kungiyar da tsoffin shugabanni da Negreira ana zargin su da laifin rashawa, karya ka’ida da kuma harkar kasuwancin karya.

Hakan ya faru ne kwanaki Kadan da shugaban na Barcelona Joan Laporta ya karyata cewa, kungiyar tasu ta bawa alkalan Wasanni kudi.

Shugaban gasar Laliga JavierTebas a nasa bangaren yace, Laporta din ya kamata yayi murabus daga mukaminsa tunda ya kasa fito yayi bayanin yaddda musayar kudin ta kasance.

Tun farko dai wani gidan rediyo mai suna Ser Catalunya ne ya fara bayyana cewa, hukumar karbar haraji sun gudanar da bincike akan kamfanin Negreira Dasnil 95.

Leave a Reply

%d bloggers like this: