Rundunar yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da kubutar da wani dan jarida da aka yi garkuwa shi a makon da ya gabata wato Seun Oduneye.

An yi garkuwa da shi a ranar Alhamis din da ta gabata ne a yayin da yake kan hanyar zuwa Ijebu Ode daga Abekuta a cikin motarsa kirar Toyota.


An rawaito cewa an yi garkuwa da dan jaridar ne da misalin karfe 7;50 na yamma a mota sai yan bindiga suka bude masa wuta tare da tsayar da shi.
Sai dai kamar yadda majiya ta bayyana yan garkuwa sun nami matarsa a waya domin biyan naira miliyan 30 don fansar mijinta.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi a yau Litiinin ya bayyana cewa dan jarida Oduneye ya shaki iskasar yanci.
Oyeyemi ya ce bayan aiki da kwararru ba wadanda suka shiga dajin ba dare ba rana don ganin an kubutar da wanda aka yi garkuwa shi kuma an yi nasara.
Ya ci gaba da cewa lokacin da jami an yan sandan suka shiga dajin sun yi artabu da yan bindigan tsawon mintuna 45 ana fafatawa sai dai da suka ji ba da ma suka tsere da muggan raunuka a jiki.
Sannan suka jefar da wanda suka yi garkuwar da shi tare da rauni a jika.
Bayan sammun nasara Kwamishinan yan sandan jihar Frank Mba ya yabawa jami’an tare da jinjina musu bisa wanannan aiki da suka yi mai kyau.
Daga karshe CP Frank Mba ya ce yana mai rokon duk wanda ya samu rauni a yayin fafatawar da aiki tsakanin yan sanda da yan bindiga a kauyen yayi saurin sanarwa.
Ya ce yan bindiga su bar jihar Ogun don kuwa sun shirya yaki da su.