Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kubutar da wasu mutane 14 da aka yi garkuwa da su a jihar wadanda suka shafe tsawon kwanaki 14 a daji.

 

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Mahammadu shehu shi ne ya bayyana haka ga manenma labarai in da ya ce wadanda aka yi garkuwa da su sun shafe sama watanni biyu a wajen yan garkuwa.

 

Ya ce kwararru daga cikin jami an yan sanda hadi da yan bijilanti su ne suka shiga dajin dake kusa da Munhaye tare da samun nasara a yunkurin bayan kama shugaban su na yankin Dogo Sule.

 

Cikin wadanda aka kubutar akwai manyan mutane Maza biyu da mata bakwai da yara biyar yan shekaru biyu cikin 14.

 

Su ka ce tun a ranar daya ga watan junairu shekarar 2023 wasu yan bindiga da yawan su suka shiga yankin Anguwar Mangwaro da manyan makamai a karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara inda suka sace mutane14 suna zaune a gidajen su tare da shafe kwanakin 68 a daji.

 

Tuni aka kai wadanda aka kubutar zuwa asibiti domin duba lafiyarsu daga bisani kuma aka mika su ga iyalansu a cewar.

 

Kwamishinan yan sandan jihar Kolo Yusuf ya taya wadnada su ka kubuta farin ciki bisa shakar iskar yanci sannan yan sanda za su ci gaba da tsare rayuka da dukiyoyin alumma.

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: