Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa yan kasuwar da ibtilain gobara ya shafa a kasuwannin Rimi da Singa a Kano.

Gwamnan wanda yaa aike da sakon jajen kamar yadda babban sakataren yaɗa labaransa Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu ranar Talata.
Ya ce asarar da aka yi ba iya masu shagunan ta shafa ba ta shafi dukkanin kasa baki daya ne.

Gwanna Ganduje wanda ya aike da sakon jajen ga ƴan kasuwar Kurmi, Rimi da kasuwar Singa.

Ya yi addu’ar kiayewar hakan a nan gaba.