Rundunar ‘yan sanda ta ayyana neman daya daga cikin yan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Bauchi, Yakubu Shehu, ruwa a jallo.

 

Ƴan sanda na neman Yakubu duk inda ya shiga su kama shi bisa zargin kisan kai, haɗa baki, illata mutane da kuma haifar da zaman lafiya.

 

Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da aka raɗawa suna CRO Form 5, wacce ta fito daga Ofishin babban Sufeta na rundunar ‘yan sandan ƙasar Najeriya.

 

Rundunar tsaron ta bukaci duk wanda ke da sahihan bayanan inda ɗan majalisar ya shiga ya tuntube ta, kuma ta yi alƙawarin ba da ladan miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka aka kama shi.

 

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Bauchi, Ahmed Wakil ne ya fitar da takarda ta musamman da ta ayyana neman ɗan majalisar ruwa a jallo.

 

Yakubu Shehu ya ci zaɓen ɗan majalisar wakilan tarayya karkashin jam’iyyar PRP. Kuma Ya sauya sheƙa zuwa jam”iyyar APC a shekarar 2022 daga bisani ya samu tikitin tsayawa takarar Sanata a jam’iyyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: