Aƙalla mutane goma ne ake zargi sun rasa rayuwarsu sanadin wani hari da aka kai garin Langson da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan hallaka mutane 17 kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

Shugaban ƙaramar hukumar Zangon Kataf Francis Sani ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ƴan bindigan sun kai harin ranar Talata da misalin ƙarfe tara na dare.

Da zuwansu su ka fara harbin mutane, sai dai an gani cewa yan bindigan sun sace kayayyaki yayin da daga bisani ƴan sanda su ka daƙile harin.

Baya ga mutane goma da su ka rasa rayukansu akwai da yawa da su ka jikkata a sanadin harin.

Tuni shugaban ƙaramar su ka bukaci gwamnatin Kaduna da ta ƙara yawan jami’an tsaro a yankin domin daƙile hakan

Wata ƙungiyar cigaban al’umma a yankin ta buƙaci mutanen yankunan da su kasance cikin shiri domin kare dukiyoyi da rayukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: