Farashin kayan masarufi ya karu da kashi 21.91 la’akari daa watan Janairun shekarar dda mu ke ciki.

An sake samun karuwar farashin duk da cewar a watan Janairun farashin ya yi sama sosai.
Hukumar kididdiga a Najeriya NBS ce ta fitar da saanarwar haka yau Laraba.

Sai dai taa alakanta hauhawaar farashin da ƙarancin takardun kuɗi a hannun jama’a.

Daga cikin kayayyakin da farashinsu ya hau akwai kayaan abinci da su ka shafi doya, biredi, nama, kifi da kayan ganye.
An sake samun ƙaruwar farashin kayayyakin da 0.09 la’akari da wataan Janairu.