Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce ta kammala aikin sabunta na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa da yan majalisun dokokin Najeriya a watan Fabrairu da ya gabata.

Hakan na daga cikin shirin da hukumar ta yi na tunkarar zaɓen gwamnoni a Najeriya.

Hukumar ta ɗage zaɓen da ta sanya ranar 11 ga watan Maris ɗin da mu ke ciki domin samun damar kammala sabunta na’urar.

Yayin da ya rage saura kwana uku a gudanar da zaɓen gwmanonin, hukumar zaɓen tuni ta fara raba kayayyakin aikin zaɓe mafi muhimmanci ga hukumomin kananan hukumomi a wasu jihohin.

Daga cikin jihohinnda aka raba kayayyakin akwai Kano da jihar Osun.

Matakin hakan da hukumar ta ɗauka shiri ne domin magance haifar da tsaiko ranaar zaben gwamnoni da ƴan majalisar jihohi na ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: