Wasu bankunan kasuwanci a Najeriya sun rage kuɗaɗen da su ke bai wa matafiya ƙasashen waje da na biyan kuɗin makarantar ɗalibai da kashi hamsin cikin ɗari.

A ranar Talata ne wasu bankunan su ka fara bayar da rabin kuɗin alawus da su ke bai wa matafiya da kashi hamsin.

Hakan ya faru ne sanadin karancin dalar Amurika da ake fama da ita a ƙasar.

A baya bankunan na bai wa matafiyan alawus na dala dubu huɗu kuma a yanzu su ka fara ba su dala dubu biyu.

Sai kuma ɗalibai da su ke ba su dala 14, kuma a yanzu su ka koma ba su dala 7,500.

Sannan bankunan sun buƙaci kwastomominsu da su dinga sanar da su ƙasa da mako ɗaya kafin yin tafiyarsu.

A wani saƙon da bankunan su ka aikewa da kwastomominsu sun buƙaci da ɗalibai su aike da saƙon sanarwa makonni 16 kafin lokacin biyan kudin makaranta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: