Wata babbar kotu a jihar Akwa Ibom ta yanke hukunci a kan wani mai suna Moses Abdon Edon hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yankewa Moses hukuncin ne bayan smaunsa daa laifin hallaka mahaifinsa.

Moses Abdon mai shekaru 37 a duniya, ya kashe mahaifin nasa ne shekaru takwas da su ka gabata.

Sai dai ba a iya gani kabari da gawar mahaifin nasa ba.

Alkalin kotun Justice Ezekiel Enang ya yankewa wanda ake tuhumar hukuncin ne bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatarwa kotu.

Kotun ta ya ke hukuncin ƙarƙashin dokar da ta bayar da damar kisa ta hanyar rataya ko da ba a samu hujja ba muddin aka gabatar da kwararan shaidu a kotu.

Kotun ta samu wanda ake tuhuma da hallaka maahaifinsa da gangan.

Hukumar Shari’a a jihar ce ta gabatar da karar aa gaban kotun bayan da ake zargin Moses da kisan mahaifin nasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: