Sashin hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun cafke wasu mutane biyu, Sharu Tabula da Isma’il Mangu bisa zargin yunkurin tayar da rikici a wasu sassan Kano.

DSS din tace wadanda ake zargin sun dauki hoton bidiyo dauke da miyagun kalamai, suna kuma yada su a kafafen sadarwa na zamani daban-daban.

Hukumar tace a cikin sakon nasu sun yi kira ga masu bin ra’ayinsu na siyasa da su kai harin rigima ga wadanda suka banbanta da ra’ayinsu, har kuwa jami’an tsaro yayin gudanazar da zaben gwamnoni da ‘yan majalissun jihohi ranar Asabar.

Hukumar ta kara da cewa tana sane da yunkurin da jam’iyyar take yi na nuna goyon baya ga wadanda ake zargin, na yin zanga-zanga da kuma mamaye ofisoshin wasu hukumomin tsaron a ranar Alhamis.

Wannan yana kunshe ne cikin wani bayani dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar ta DSS Peter Afunanya, wanda aka rabawa manema labarai a yau Alhamis.

Kuma yayi kira ga shugabannin jam’iyyar da su ja hankalin magoya bayansu, dan kaucewa yin abin da zai tayar da hankali da kuma karya doka, yayin zaben da kuma bayansa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa DSS din tace bayan jihar Kano ma, ta cafke irin wadannan gurbatattun mutanen masu kokarin tayar da husuma a wasu jihohin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: