Wata kungiya mai kare hakkin kiristoci a Najeriya wato Concern Christians Of Najeriya dake jihar Kaduna sun bukaci da zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya Asiwaju Bola Tinubu da ya bai’wa kungiyar manyan kujeru a gwamnatinsa.

 

Shugaban kungiyar John Audu Kwaturu ya bayyana hakan ta cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis akan bukatar ta su.

 

Kungiyar ta bayyana cewa tunda shugaba Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima musulmai ne to a warewa mabiya addinin kirista manyan kujeru guda biyu.

 

Kujerun da kungiyar ta ke nema sun hada kujerar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da kuma Sakataren gwamnatin tarayya.

 

Kungiyar ta kara da cewa bai’wa kiristoci kujerun hakan ne zai tabbatar da anyi adalci da gaskiya a wajen raba kujeru a gwamnatin ta Tinubu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: