Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kone kayyakin hukumar zabe ta kasa INEC da ke cibiyar rarraba kayayyakin zabe a Okodi da ke cikin karamar hukumar Ogbla a Jihar Bayelsa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na daren yau Asabar wanda ta kasance ranar da za a gudanar da zaben ‘yan majalisun Jihar da sauran Jihohi.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa kayan zaben na gunduma ta biyu ne da ta uku da hudu da kuma ta biyar a yankin na Ogbia,inda su ka kone kurmus bayan sanya musu wuta.

Shaidan ya kara da cewa kone kayayyakin ya haifar da cikas ga mazauna yankin a kokarin da su ke na kada kuri’a a lokacin zaben da za a gudanar dashi a ranar.

Bayan kone kayan jami’an da hukumar ta INEC ta aike mazabun domin gudanar da aikin zaben sun koma Yanagua babban birnin Jihar domin tsira da rayukansu.
A yayin jawabin sa da ya fitar da sanyin Safiyar yau Asabar Sakataren yada labaran gwamnan Jihar Daniel Alabrah ya tabbatar da faruwar lamarin.
Gwamnan Jihar ta Bayelsa Douye Diri yayi Allah wadai da harin na batagarin,tare da yin kira ga Sufeto Janar na ‘yan sanda na Kasa da kwamishinan ‘yan sandan Jihar da su tabbatar da zaman lafiya a Jihar.
Anasa bangaren shugaban sashin yada labarai na hukumar ta INEC a Jihar Wilfred Ifogah ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar Lamarin,inda ya ce nan bada dadewa ba za su fitar da sanarwa nan gab