Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bai’wa ‘yan Najeriya shawara cewa kowanne ya zabi ra’ayinsa a lokacin zabe,inda ya ce zamanin sayan kuri’a ya wuce a yanzu.

Mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan shugaban ya kada kuri’a a mazabar sa da ke Jihar Katsina.
Shugaba Bujari ya bayyana cewa a halin da ake ciki a yanzu a Najeriya al’umma sun waye da zabin ra’ayinsu a lokacin zabe.

Shugaban ya ce a yanzu mutane ko da an basu kudi da nufin sayan kuri’a su na amsa amma kuma su na zaben ra’ayinsu.

Buhari ya kuma jinjinawa kafafen yada labarai bisa rawar da su ka taka wajen wayar da kan al’umma domin su san hakko kinsu a matsayin su na ‘yan kasa.tare kuma da samar musu da kafar da za su kalubaanci shugabanni akan alkawuran da su ka daukar musu.