Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya buƙaci ƴan jam’iyyar NNPP da su daakatar d ayin tattalin murna a fadin jihar.

A wata sanarwa da mia magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ya hori mutanen da su koma domin ci gaba da addu’a.

Sanarwar da aka fitar yau Labara ta ce a wannan lokaci ya dace a yi addu’a tare da nuna godiyarsu ga Allah.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ce ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka yi a makon jiya.

A wani labarin kuma jamiyyar APC a Kano ta gudanar da zanga-zanga tare da watsi da sakamakon da aka ayyana.

Jagororin jam”iyyar ne su ka yi tattaki tare da yin zanga-zanga zuwa ofisoshin hukumar a Kano.

Jamiyyar ta bukaci hukumar ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Ko aa jiya sai da jamiyyar APC ta jaddada matsayarta a wani taron mamema labarai da ta yi a ofishin yakin meman zabenta a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: