Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan kasuwa da ke kara farashin kayayyai saboda zuwan azumi tare da shawartarsu da su daina domin hakan ba abune mai kyau kana ya saba da koyarwar musulunci.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar kasa game da shigoawar watan Ramadan.
Shugaban ya kuma shawarci musulmin Najeriya da su suyi amfani da lokacin wajen haskaka kyawawan dabi’un addinin Islama a mu’a malolinsu ba iya fatar baki ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar ta ce ya kamata musulmi su yi amfani da lokacin wajen bayyana kyawawan dabi’un addinin musulunci kamar su tausayawa da kanar juna.

Sanarwar ta bayyana cewa shugaba Buhari na sane da yadda wasu ‘yan kasuwa ke kara farashin kayyayaki ciki harda kayan abinci a cikin watan ramadan wanda hakan ya sa6a da koyarwar addinin Islama.