Babban bankin Najeriya CBN ya tabbatar da fito da takardun kudi daga Asusun bankin tare da bai’wa bankunan fadin kasar domin ganin an samu wadatuwar kudaden a hannun al’ummar kasar.

 

Daraktan yada labara bankin Dr Isa Abdulmumin ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a birnin tarayya Abuja.

 

Daraktan ya kara da cewa bankin ya kuma bai’wa bankunan umarnin gudanar da ayyuka a ranakun Asabar da Lahadi.

 

Dr Isa ya bayyana cewa CBN ya bai’wa bakunan isassun kudade domin ci gaba da rabawa al’umma.

 

Isa ya ce CBN ya kuma bai’wa bankunan umarnin sanya kudade a injinan cirar kudade na ATM, tare da gudanar da ayyuka a ranakun karshen mako.

 

Daraktan ya kara da cewa gwamnan babban bankin Godwin Emefile da kanshi zai jagoranci tawaga domin duba ayyuka da aka bai’wa bankunan ‘yan kasuwa umarnin gudanarwa.

 

Daga karshe Dr Umar ya bukaci ‘yan Najeriya da su kara hakura domin komai ya kusa zuwa karshe sakamakon fito da kudaden da CBN yayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: