Gwamnatin jihar Jigawa ta ragewa ma’aikatan Jihar lokacin tashi daga aiki tsawon watanni biyu sakamakon shigowar watan Azumin Ramadan.

Jami’in hulda da jama’a na Ofishin shugaban Ma’aikatan Jihar Alhaji Isma’il Dutse ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aka aikewa da manema labarai a garin Dutse da ke Jihar.


Kakakin ya ce ma’aikata a Jihar za su dinga zuwa aiki karfe 9 na safiya zuwa karfe uku na yammacin kowacce rana daga Litinin zuwa Alhamis.
Alhaji Isma’il ya ce a baya ma’aikatan su na zuwa aiki ne karfe 8 na safiya su tashi karfe 5 ,inda aka rage musu lokutan zuwa aiki da kuma tashi daga aiki albarkancin shigowar watan Azumin Ramadan.
Kakakin ya kara da cewa gwamnatin Jihar ta dauki matakin hakan ne domin bai’wa ma’aikatan damar gudanar da ibada a cikin watan.
Isma’il Dutse ya ce Ma’aikatan za kuma su samu damar yiwa Jihar Addu’o’in zaman Lafiya tare da bunkasar tattalin arziki a Jihar.
A nasa bangaren Shugaban ma’aikatan Jihar Hussaini Kila ya bayyana cewa a ranar Juma’a kuma ma’aikatan za su ci gaba da aiki da misalin karfe 9 na safiya zuwa karfe 1:00 na rana kamar yadda aka saba.